26 Afirilu 2021 - 13:04
​Rikicin Siyasa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 4 A Somalia

Akalla mutane hudu aka tabbatar da muturawarsu a kasar Somalia, biyo bayan wani rikicin siyasa da ya barke a kasar, sakamakon sake dage lokutan gudanar da zabuka.

ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, an yi harbe-harbe da bindigogi a birnin Mugadishu fadar mulkin kasar Somalia a jiya Lahadi, biyo bayan sanarwar da aka bayar ta sake dage lokacin gudanar da zabe a kasar.

Magoya bayan manyan ‘yan siyasar kasar ne dai suka yi harbe-harbe a tsakaninsu, lamarin mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a birnin Mugadishu Ahmad Bashan ya ce ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 4 da kuma jikkatar wasu.

Shugaban kasar Somalia Muhamamd Abdullah Farjamo ya sanar da kara wa kansa shekaru 2 a kan kujerar shugabancin kasar, inda ya mika batun ga majalisar wakilai kuma ta amince da hakan, yayin da ya kewaye majalisar dattijai ba tare da ya nemi izininta ba.

Wannan mataki dai ya fusakanci kakkausar suka daga bagarorin ‘yan adawa a kasar, kamar yadda wasu bangarori na kasashen ketare ma suka yi Allawadai da hakan, daga cikin har da Kungiyar Tarayyar Turai, da suke ganin hakan a matsayin wani mataki da zai kara dagula lamurra a kasar ta Somalia.

Tun a ranar 8 ga watan Fabrairun da ya gabata ne wa’adin mulkin Muhammad Abdullah Farjamo ke kawo karshe, amma saboda kasa shirya gudanar da zabuka, ya ci gaba da kasancewa a kan kujerarsa.

342/